-
Mutane 87 Ruwan Sama Ya Kashe A China
Jul 23, 2016 13:03Hukumomi a kasar China sun ce mutane 87 ne suka rasa rayukan sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da aka samu a 'yan sa'o'in da suka gabata a yankin tsakiyar gabashin kasar.
-
Adadin Mutanen Da Suka rasu A Harin (IS) A Afganistan Ya Kai 80
Jul 23, 2016 12:24Kungiyar 'yan ta'ada ta (IS) ta dau alhakin kai wani mumunan hari da ya yi sanadin rasuwar mutane kimanin 80 da raunana wasu a kalla 231 a birnin Kabul na kasar Afganistan.
-
Shugaban Kasar Masar Ya Bayyana Aniyarsa Ta Warware Matsalar Palasdinu
Jul 23, 2016 01:20Shugaban kasar Masar ya bayyana aniyarsa ta dukufa a fagen ganin ya warware matsalar al'ummar Palasdinu.
-
Masarautar Ali-Saud Ta Haramta Wa Maniyyatan Syria Zuwa Aikin Hajjin Bana
Jul 22, 2016 12:34Sarakunan masarautar iyalan gidan Saud sun hana musulmi maniyyata daga kasar Syria zuwa aikin bana, ta hanyar hana su izinin shiga kasar (visa) ba tare da bayyana wani dalili na yin hakan ba.
-
Jami'an Tsaron Masarautar Bahrain Sun Hana Gudanar Da Sallar Juma'a
Jul 22, 2016 10:31Mahukuntan kasar Bharian sun hana al'ummar yankin Diraz gudanar da sallar Juma'a a yau tare da hana limamin masallacin Juma'a na yankin Sheikh Muhammad Sanqur isa masallacin.
-
Yanayin Tsaro Da Koma Harkokin Siyasa A Dai Dai LokacinDa Sojojin Iraqi Suke Kokarin Qatar Birnin Musil.
Jul 22, 2016 01:07Amurla zata aike da karin sojoji zuwa kasar Iraqi don kwatar birnin Musil daga hannun Daesh
-
Tsagerun Yahudawan Sahayoniyya Sun Sake Mamaye Masallacin Qudus
Jul 21, 2016 14:25Tsagerun Yahudawan Sahayoniyya sun sake kai farmaki kan Masallacin Aksa da ke birnin Qudus a yau Alhamis, inda suka kutsa kai cikin Masallacin ta Bubul-Magharibah kuma sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun hana duk wani bapalasdine kusantar Masallacin.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Dakatar Da Bude Wuta A Arewacin Kasar Siriya
Jul 21, 2016 13:33Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci dakatar da bude wuta a lardin Halab da ke arewacin kasar Siriya tsakanin sojojin gwamnatin da gungun 'yan ta'adda da nufin samun damar isar da kayayyakin jin kai a yankunan lardin.
-
Jiragen Saman Yakin Saudiyya Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Kasar Yamen
Jul 21, 2016 13:22Jiragen saman yakin masararutar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan yankin arewacin kasar Yamen inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu adadi na daban.
-
Mahukuntan Bahrain Na Ta Kara Kaimi Wajen Cin Zarafin Al'ummar Kasar
Jul 21, 2016 06:27Masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain na ci gaba da daukar matakan cin zarafi a kan manyan malamai da kuma masu fafutukar kare hakkin bil adama da sauran al'ummar gari.