-
Dakarun Tsaron Yemen Sun Halba Makami Mai Linzami Cikin Kasar Saudiya
Jul 18, 2018 13:44A matsayin mayar da martani kan irin ruwan bama-baman da jiragen yakin kawancen Saudiya ke yi a kasar, Dakarun tsaron yemen sun halba makami mai linzami zuwa birnin Najran na kasar Saudiya
-
An Gano Tarin Makaman Isra'ila A Yankunan Da Aka Tsarkake Na Siriya
Jul 18, 2018 13:43Dakarun tsaron Siriya sun gano tarin makaman Isra'ila a hanun 'yan ta'adda yayin tsarkake yankin Akrab na gefen kudancin Hamah.
-
Shugaban Kungiyar Ansarullah Ya Ce Yana Iya Amincewa Da Sanya Idon MDD A Hudaida Amma Da Sharadi
Jul 18, 2018 07:38Shugaban kungiyar Ansuraullah ta kasar Yemen Abdul-Malik Badruddin Huthi ya bayyan cewa ba zai ki bukatar MDD ta sanya ido a kan lamuran da ke faruwa a birnin Hudaida na bakin ruwa ba amma da sharadin kawancin kasashen da suke yakarsa kasar su dakatar da hare haren da suke kaiwa a kan birnin na Hudaida.
-
An Zargi Birtaniya Da Hannu A Keta Hakkin Dan'adama A Kasar Bahrain
Jul 18, 2018 01:47Kungiyar da take fada da cinikin makamai a duniya ya ce; Birtaniya tana kau da ido akan yadda ake take hakkin dan adama a kasar Bahrain
-
Gwamnatin Masar Ta Rufe Mashigar Rafah Da Ke Tsakanin Kasarta Da Yankin Zirin Gaza Na Palasdinu
Jul 17, 2018 14:35Gwamnatin Masar ta rufe mashigar Rafah da ke tsakanin kan iyakar kasarta da yankin Zirin Gaza na Palasdinu lamarin da zai kara wurga al'ummar yankin Zirin Gaza cikin mawuyacin hali.
-
Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Kashe Fararen Hula A Lardin Hudaidah Na Kasar Yamen
Jul 17, 2018 14:34A ci gaba da luguden wuta da jiragen saman yakin masarautar Saudiyya suke yi a lardin Hudaudah da ke yammacin kasar Yamen sun yi sanadiyyar mutuwar fararen hula akalla 7 a yau Talata.
-
Jami'an Tsaron Iraki Fiye Da 50 Ne Suka Jikkata A Ci Gaba Da Zanga-Zangar Da Al'umma Ke Yi A Karbala
Jul 17, 2018 14:31Ministan harkokin cikin gidan kasar Iraki ya sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar fiye da 50 ne suka jikkata a ci gaba da zanga-zangar da al'ummar garin Karbala ke yi kan nuna rashin amincewarsu da irin mawuyacin halin da suke ciki a fagen rayuwa.
-
Kungiyar Hamas Ta Gargadi HKI A Dai-Dai Lokacinda Take Kara Kuntatawa Mutanen Yankin Gaza
Jul 17, 2018 07:26Kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da HKI da makamai ta gargadi HKI kan matakan da take dauka na rufe hanyoyin shigar makamashi da abinci zuwa yankin Gaza.
-
Jiragen Yakin Kawancen Amurka Na Ci Gaba Da Kai Hari A Siriya
Jul 16, 2018 13:43Jiragen yakin kawancen Amurka sun yi ruwan bama-bamai kan kauyen Assusa na jihar Dairu-Zur tare da kashe fararen hula a wannan Litinin.
-
Yemen: An Kashe Sojojin Saudiyya 4 Akan Iyaka
Jul 16, 2018 02:21Sojojin Saudiyyar 4 ne su ka halaka a wani taho mu gama da sojojin kasar Yemen