-
Larabawa Sun Jaddada Yin Watsi Da Matakin Amurka Kan Qudus
Apr 16, 2018 01:48Taron kasashen larabawa da ya gudana a birnin Dammam na kasar Saudiyya, ya jaddada yin watsi da matakin shugaba Donald Trump na Amurka na ayyana Qudus a matsayin babban birnin mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila.
-
Nasrallah: Harin Wuce Gona Da Iri Kan Siriya Ya Gaza Cimma Ko Guda Daga Cikin Manufofinsa
Apr 15, 2018 12:53Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah, ya jinjinawa namijin kokarin da sojojin Siriya suka nuna wajen mayar da martani ga harin wuce gona da irin Amurka da kawayenta kan Siriya yana mai cewar harin ya gaza wajen cimma manufofin da ake son cimmawa don biyan bukatun 'Isra'ila' da wasu kasashen larabawan yankin.
-
Yemen: An Kashe 'Yan Koran Saudiyya 34
Apr 15, 2018 06:38Majiyar sojan Yemen ce ta sanar da kashe 'yan koran Saudiyyar 34 a yankin Ta'iz da Jaufa a al-baidha'a.
-
Kwamitin Tsaro Na MDD Ya Ki Yin Allawadai Da Hare-Haren Da Aka Kaiwa Kasar Siriya
Apr 15, 2018 02:03Komitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya yi watsi da bukatar kasar Rasha na yin allahwadai da hare-haren da kasashen Amurka, Faransa da Britania suka kai kan wasu wurare a kasar Siriya a ranar Asabar.
-
Falastinawa 4 Sun Yi Shahada A Hare-Haren Da Isra'ila Ta Kai Yau A Gaza
Apr 14, 2018 13:53Sakamakon hare-haren da jiragen yakin Isra'ila suka kaddamar a kan al'ummar Gaza a yau, Palastinawa 4 ne suka yi shahada wasu kuma suka samu raunuka.
-
Siriya Ta Ce Hare-haren Da Aka kai Mata, Keta Dokokin Kasa Da Kasa Ne
Apr 14, 2018 01:58Gwamnatin Siriya ta danganta hare haren sojin da kasashen Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai mata a cikin daren jiya da keta dokokin kasa da kasa da hurimin da kasar take da shi.
-
Gaza: Palasdinawa 30 Sun Jikkata daga harin Sojojin Sahayoniya
Apr 13, 2018 14:50Juma'a ta uku kenan da al'ummar palasdinu take gudanar da Zanga-zangar hakkin komawa gida akan iyakar Gaza da palasdinu da ke karkashin mamaya
-
Abdulmalik Badruddin al-Huthy: Manufar Amurka Shi Ne Shimfida Ikonta A Gabas Ta Tsakiya
Apr 13, 2018 14:48Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen wanda ya gabatar da jawabi sa'o'i kadan da su ka gabata, ya ce; Harin 11 ga watan Satumba wata dama ce da Amurkan ta yi amfani da ita domin shimfida ikonta a gabas ta tsakiya
-
Sayyid Hassan Nasarallah: Harin Da 'Yan Sahayoniya Suka Kai A Tifur Wauta Ce Ta Tarihi
Apr 13, 2018 14:46Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya gabatar dazu.
-
Jami'an Tsaron Isra'ila Sun Kai Farmaki Kan Palastinawa
Apr 13, 2018 06:49Jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki kan matasan Palastinawan da suka taru a sansanin Auda dake gabashin Khan Yunus