Venezuela Za Ta Gabatar Da Sabuwar Shawarar Karfafa Kasuwar Man Fetur
(last modified Sun, 21 Feb 2016 10:42:13 GMT )
Feb 21, 2016 10:42 UTC
  • Venezuela Za Ta Gabatar Da Sabuwar Shawarar Karfafa Kasuwar Man Fetur

Sakamakon ci gaba da fadin farashin man fetur a kasuwar duniya, shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewar kasarsa tana shirin gabatar da wasu sabbin shawarwari ga kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC da ma wadanda ba na OPEC din ba kan yadda za a karfafa kasuwar man.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar shugaba Maduro ya sanar da hakan ne a wani jawabi da yayi inda ya ce suna shirin gabatar da sabbin shawarwari kan hanyoyin da za a bi wajen daidaita kasuwar man a duniya, inda ya ce wajibi ne kasashen da suke samar da man fetur din sun zamanto su ne masu ayyana yadda farashin mai din zai kasance.

Cikin 'yan kwanakin nan dai farashin man fetur yayin wani irin faduwar da aka jima ba a ga irinsa ba lamarin da ya sanya kasashe da dama musamman masu arzikin man fetur din cikin tsaka mai wuya na tattalin arziki, inda da dama suke dora alhakin hakan a kan kasar Saudiyya wacce ta a watannin baya ta yi sanadiyyar faduwar farashin man da nufin karya tattalin arzikin kasashen Rasha da Iran.