An Hallaka Wasu Kwamandodin Al'Qaida A Yemen
Rahotanni daga Yemen na cewa wani harin jirgi marar dreba ya hallaka wasu kwamandodin kungiyar Al'Qaida biyu a tsakiyar kasar.
Wani jami'in gwamnati a yankin ya shaidawa kanfanin dillancin labaren faransa na AFP cewa an hallaka mutanen ne biyu a ranar Alhamis data gabata a lokacin da suke shakatawa karkashin wani icce a lardin Rada dake yankin Baida a tsakiyar kasar.
koda yake labarain bai bayyana sunan kwamandodin da aka hallaka ba, amma majiyar ta ce Amurka ce kadai keda nau'in jiragai marar matuka dake iya kai wannan harin.
kungiyar Al'Qaida reshen Yemen wato (Aqpa) ita ce kungiyar 'yan ta'adda mafi hadari a idon Amurka a fadin duniya.
Rahotanni daga yankin sun nuna cewa ko a makon daya gabata Amurka ta kai hari a wannan yankin saidai ba tare da yin karin haske ba.