Putin: Rasha Tana Cikin Shirin Fuskantar Duk Wata Barazana
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewar sojojin kasarsa suna cikin shirin ko ta kwana wajen tinkarar duk wata barazana da za ta iya fuskanta daga waje.
Tashar talabijin Al-Mayadeen ta kasar Labanon ta bayyana cewar: Shugaba Vladimir Putin na kasar Rashan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da membobin majalisar koli ta tsaron kasar Rashan da manyan kwamanodojin sojin kasar inda ya ce sojojin kasar suna cikin shirin ko ta kwana wajen tinkarar duk wata barazana.
Shugaba Putin ya kara da cewa sojojin kasar Rashan suna da dukkan karfin da ake bukata wajen tinkarar duk wata barazana.
Shugaba Putin din dai yana mayar da martani ne ga maganganun da wasu jami'an kasashen Turai da ma na Amurka suke yi ne dangane da irin karfin da kasar Rashan take da shi da kuma irin tasirin da take ci gaba da samu a yankuna daban daban na duniya.