An bukaci Isra'ila da ta fice daga tsaunukan Golan
https://parstoday.ir/ha/news/world-i14770-an_bukaci_isra'ila_da_ta_fice_daga_tsaunukan_golan
Majalisar Dinkin Duniya ta sake fitar da wani kudirin inda ya bukaci haramcecciyar kasar Isra'ila da ta fice daga tsaunukan Golan
(last modified 2018-08-22T06:59:20+00:00 )
Dec 03, 2016 07:51 UTC
  • An bukaci Isra'ila da ta fice daga tsaunukan Golan

Majalisar Dinkin Duniya ta sake fitar da wani kudirin inda ya bukaci haramcecciyar kasar Isra'ila da ta fice daga tsaunukan Golan

Tashar Telbijin din Press Tv dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa kasashen 37 ne suka gabatar da wannan bukata sannan kuma ya samu amince daga kusan dukkanin manbobin majalisar, shi dai wannan kudiri ya bukaci Haramcecciyar kasar Isra'ila da ta janye sojojin ta daga tsaunukan Golan da ta mamaye tun daga shekarar 1967 har zuwa yanzu.

Haramcecciyar kasar Isra'ilan na ci gaba da shan suka saboda rashin mutunta kudiri mai lamba 497 na kwamitin tsaron MDD wanda aka samar a shekarar 1981 da ya bukaci HKI ta janye daga wannan yanki.

Sanarwa da MDD ta fitar ta ce ci gaba da mamaye tsaunukan Golan daga bangare HKI take dokokin kasa da kasa ne, kuma dukkanin manbobin Majalisar sun yi kakkausa suka ga Gwamnatin Haramcecciyar kasar Isra'ilan.