Kasashen Amurka Da Birtaniyya Na Leken Asirin Shugabannin Afirka
(last modified Fri, 09 Dec 2016 06:37:37 GMT )
Dec 09, 2016 06:37 UTC
  • Kasashen Amurka Da Birtaniyya Na Leken Asirin Shugabannin Afirka

Jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta buga wani labari da ke cewa tana dauke da wasu takardun shaida da ke nuni da cewa Ma'aikatun Leken Asirin Amurka da na Birtaniya suna gudanar da leken asiri kan shugabanni da manyan 'yan kasuwar 20 na Afirka.

Kafar watsa labaran Africanews ya bayyana cewar jaridar ta ce bisa ga bayanan da ta samu ta hannun tsohon jami'in hukumar tsaron cikin Amurka Edward Snowden wanda a halin yanzu yake gudun hijira a kasar Rasha sun bayyana cewar Amurka da Birtaniyya sun sanya nahiyar Afirka karkashin na'urorinsu na leken asiri.

Jaridar ta kara da cewa dukkanin wadanda Amurkawa da Birtaniyyan suka cikin jerin sunayen leken asirin na su sun hada da shugabanin kasashe da shugabannin gwamnati, jagorin 'yan tawaye da sauran manyan 'yan kasuwa na Afirkan.

Jaridar ta ci gaba da cewa alal akalla kasashe 20 na Afirka ne suke karkashin wannan leken asirin na Amurka da Birtaniyya da suka hada da kasashen Dimokradiyyar Kogo, Angola, Togo, Sierra Leone, Guinea, Ghana da kuma Nijeria.

Bayanan sun kara da cewa ana amfani ne da kamfanonin wayar tarho na wadannan kasashe wajen gudanar da irin wadannan leken asirin.

Wannan dai ba shi bayani masu muhimmanci suke fitowa da suke nuni da irin yadda alala akalla wadannan kasashen na Yammaci suke gudanar da leken asirin a kan wasu kasashen Afirkan kai hatta ma dai da wasu na nahiyar Turai da ake ganinsu a matsayin manyan kawayensu ba.