Sojojin Siriya Sun Fatattakin 'Yan Ta'addan Da'esh Daga Palmyra Na Siriya
Rahotanni daga kasar Siriya sun bayyana cewar sojojin Siriya da suke samun daukin jiragen yakin kasar Rasha sun fatattaki 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh da suka yi kokarin sake kwace garin Palmyra mai tsohon tarihi daga hannun dakarun Siriyan a jiya.
Kungiyar kare hakkokin bil'adama ta Syrian Observatory for Human Rights ta bayyana cewar hare-haren da jiragen yakin Rasha suke kai wa ta sama bugu da kari kan wutar da sojojin Siriya suke yi ta kasa ya tilasta wa 'yan ISIS (Da'esh) din ranta cikin na kare daga garin na Palmyra bayan sun shige shi na 'yan wasu awoyi a jiya.
Kungiyar ta kara da cewa an kashe wani adadi mai yawa na 'yan ta'addan Da'esh din yayin wadannan hare-hare.
A ranar Alhamis din da ta gabata ce dai 'yan kungiyar ta'addancin ta Da'esh suka fara kaddamar da hare-hare da nufin kwato garin na Palmyra da ke yammacin lardin Homs.