Burtaniya ta kare ta'addancin Saudiya a Yemen.
(last modified Mon, 12 Dec 2016 05:19:58 GMT )
Dec 12, 2016 05:19 UTC
  • Burtaniya ta kare ta'addancin Saudiya a Yemen.

Ministan tsaron Burtaniya ya kare ta'ddancin da magabatan Saudiya ke yi a kasar Yemen

Ministan tsaron kasar Burtaniya Michel Fallon ya bayyana cewa hare-haren da kasar Saudiya ke kaiwa kasar Yemen wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyar mutuwar Duban Mutane, Hakkin Saudiya ne.

A yayin da yake bayyana kusancin alakar dake tsakanin kasar sa da magabatan birnin Riyad,Mr Fallon ya ce manufar hare-haren da Saudiya ke kaiwa kasar Yemen kare kai da kuma warware rikicin kasar ta yemen ne.

Wannan sanarwa na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Ministan harakokin wajen Burtaniyar Boris Johnson ya sanar da cewa Gwamnatin Saudiya na amfani da sunan musulinci wajen kare manufofinta na Siyasa da kuma shelanta yaki a gabas ta tsakiya.

Tun daga watan Maris din shekarar 2015 ne kasar Saudiya ta fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Al'ummar kasar Yemen bisa da'awar medo da halarcecciyar Gwamnati ta Shugaban kasar da ya yi murabus Abdu Rabbahu Hadi Mansur, ya zuwa yanzu sama da Yamaniyawa dubu 11 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu dabai na daban suka jikkata.