Obama Yayi Watsi Zargin Juya Wa Yahudawa Baya Da Ake Masa
(last modified Tue, 10 Jan 2017 17:03:39 GMT )
Jan 10, 2017 17:03 UTC
  • Obama Yayi Watsi Zargin Juya Wa Yahudawa Baya Da Ake Masa

Shugaban kasar Amurka Barack Obama yayi watsi da zargin da wasu 'yan jam'iyyar Republican ta kasar da kuma firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu suke masa na juya wa yahudawa baya, ind ya ce hakan wata farfaganda ce kawai da nufin bata masa suna.

Shugaba Barack Obaman ya bayyana hakan cikin wata hira da yayi da tashar talabijin din haramtacciyar kasar Isra'ilan da za a watsa ta gaba daya a ranar Alhamis mai zuwa inda ya ce zargin juya wa yahudawa baya da wasu 'yan jam'iyyar Republican da kuma Netanyahu suke masa zargi ne kawai na siyasa da babu gaskiya cikin hakan.

Shugaba Obama ya ce wadannan mutanen suna yin hakan ne kawai don kawar da hankulan mutane daga batun ci gaba da gina matsugunan yahudawa, amma ba su da wata hujja ta fadin wannan magana ta su.

Tun dai bayan da gwamnatin Amurkan ta ki hawa kujerar naki dangane da wani kuduri da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a kwanakin baya inda yayi Allah wadai da haramtacciyar kasar Isra'ila, tun a wannan lokacin Netanyahu da wasu 'yan jam'iyyar Republican din suka ta zargin shugaba Obaman da juya wa yahudawan baya.