Sojojin Yemen Sun Harbo Wani Jirgin Yakin Sojojin Hayan Saudiyya
Sojojin Yemen tare da dakarun kungiyar Ansarullah sun sami nasarar harbo wani jirgin yakin Saudiyya da kawayenta samfurin Apachie a lardin Ta'iz da ke kudu maso yammacin kasar Yemen din.
Tashar talabijin din Al-Masira ta kasar Yemen din ta ba da rahoton cewa sojojin Yemen din da dakarun na Ansarullah, a ci gaba da mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin sojojin Saudiyya da sojojin hayanta, sun sami nasarar harbo wani jirgin saman yaki da ya shigo yankin na Ta'iz.
Har ila yau sojojin kasar Yemen din sun sami nasarar hana sojojin sa kai din shigowa da kuma hare-haren da suke son kai wa yankin Al-Jadid da Al-Kadha inda suka fatattake su.
Sojojin na Saudiyya da kawayenta dai sun kaddamar da wasu munanan hare-hare ne cikin kwanakin nan da nufin kwace yankin Bab al-Mundhab.