An yi alawadai da harin ta'addancin da aka kai kasar Iraki
Kwamitin tsaro na MDD ya yi alawadai kan harin ta'addancin da aka kai kasar Iraki
A cikin wata sanarwa da ya fitar Kwamitin tsaron MDD ya yi alawadai da duk wani nau'i na ta'addanci, inda ta ce ta'addanci babbar barazana ne ga sulhu da kuma tsaron Duniya, manbobin Kwamitin sun bayyana cewa ya zama dole a hukunta wadanda suka kirkiro 'yan ta'adda da masu taimaka masu da kudade.
Har ila yau manbobin Kwamitin tsaron na MDD sun bukaci dukkanin kasashe da su taimakawa kasar Iraki a yakin da take yi da ta'addanci.
A ranar 16 ga watan favrayu da muke ciki ne wata Mota shake da bama-bamai ta tarwatse a kudu maso yammacin birnin Bagdaza,lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane 45 tare da jikkata wasu 56 na daban.
A watan Favrayun da ya gabata, hare-haren ta'addanci, rikici da kuma fada da makami ya yi dauki rayukan Mutane 382 tare da yin sanadiyar jikkatar wasu 908 na daban a kasar ta Iraki.