Kwamitin Tsaro Na Taron Gaggawa Kan Batun Koriya Ta Arewa
(last modified Wed, 08 Mar 2017 17:47:42 GMT )
Mar 08, 2017 17:47 UTC
  • Kwamitin Tsaro Na Taron Gaggawa Kan Batun Koriya Ta Arewa

Kwamitin tsaro na MDD na wani taro domin duba matakan dauka a kan Koriya ta Arewa bayan gwajin makamai masu linzami guda hudu data yi a baya bayan nan.

Kasar Sin dake dasawa da gwamnatin Pyongyang, ta gabatar da wata shawara a yau Laraba wace take ganin zata sassauta zamen tankiya da ake ciki a yankin.

A shawarar data gabatar kasar Sin ta ce Koriya ta Arewa na iya dakatar da shirinta na nukiliya idan Amurka ta dakatar da atisayan soji da take a kudanci.

Kasashen Faransa da Japon da kuma Ingila da aka bukaci ra'ayoyinsu kan wannan shawara sun ce maganar karshe na ga kasar Koriya ta Arewar.

Jakadan Biritaniya a MDD Matthew Rycroft ya bayyana cewa atisayan da Amurka da Koriya ta Kudu kayi ba barazana ce ba ga zamen lafiya da tsaro a duniya, yayin da jakadan Faransa a MDD ya ce Koriya ta Arewa ce ya kamata ta gwada da gaske take tana son tattaunawa.