Amnesty International Ta Soki Amurka Da Birtaniyya Saboda Take Hakkokin Bil'adama
(last modified Thu, 23 Mar 2017 16:33:37 GMT )
Mar 23, 2017 16:33 UTC
  • Amnesty International Ta Soki Amurka Da Birtaniyya Saboda Take Hakkokin Bil'adama

Kungiyar kare hakkokin bil'adama ta kasa da kasa Amnesty International ta zargi gwamnatocin Amurka da Birtaniyya da yin karen tsaye ga hakkokin bil'adama a kasar Yemen sakamakon ci gaba da sayar wa kasar Saudiyya da makamai wadanda take amfani da su wajen kai hari kasar Yemen.

Mataimakiyar daraktan bincike na yankin Gabas ta tsakiya da Arewacin Afirka Lynn Maalouf  ce ta bayyana hakan a yau Alhamis a kasar Labanon inda ta ce ci gaba da sayar da makamai da biliyoyin daloli da gwamnatocin Amurka da Birtaniyya suke yi wa gwamnatin Saudiyya yin karen tsaye ne ga hakkokin bil'adama don kuwa gwamnatin Saudiyya tana amfani da wadannan makamai wajen kai hare-hare kan fararen hula.

Lynn Maalouf ta kara da cewa: Tun daga lokacin da Saudiyya ta kaddamar da hare-hare kan kasar Yemen, Amurka da Birtaniyya sun sayar wa Saudiyya makaman da kudinsu ya kai dala biliyan biyar lamarin da yayi sanadiyyar tarwatsa rayuwar dubun dubatan fararen hulan kasar Yemen.

Jami'ar kungiyar Amnesty International din ta kara da cewa wadannan hare-haren Saudiyya sun yi sanadiyyar sanya 'yan kasar Yemen miliyan 18 cikin halin neman taimako na gaggawa.