Shugaba Rauhani Na Iran Ya Isa Birnin Moscow Na Rasha
Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani ya isa birnin Moscow na kasar Rasha a yammacin yau, a ziyarar kwanaki biyu da zai gudanar a kasar bisa gayyatar da shugaba Putin ya aike masa.
Shugaba Rauhani ya isa babban filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Moscow a yammacin yau, inda a daren yau zai gana da Firayi ministan kasar ta Rasha Dmitry Medvedev.
A safiyar gobe Talata kuma zai gabatar da jawabi a babbar jami'ar Moscow ga malaman jami'ar da kuma masana da za su halarci wurin, inda jami'ar za ta bayar da digirin digirgir na girmamawa ga shugaba Rauhani.
Haka na kua a gobe ne da rana zai isa fadar shugaba Vladmir Putin, inda za su gudanar da tattaunawa a kan batutuwa da dama da suka shafi alaka a tsakanin Iran da Rasha, musamman a bangarorin harkokin tattalin arziki da cinikayya da sauran ayyuka a fagen ilimi da kuma tsaro, haka nan kuma za su duba sauran batutuwa da suka shafi ayyuka na hadin gwiwa da suke yi tare musamman a fagen yaki da ta'addanci a Syria.