De Mustura:Kwamitin Tsaron MDD Zai Yi Zama Kan Kasar Siriya
Wakilin Musamman na MDD kan Kasar Siriya ya ce: Kwamitin tsaro zai yi zama kan harin makami mai guba da aka kai a Arewa maso yammacin Siriya.
A yayin ganawarsa da Shugabar Ofishin kare manufofin ketare ta kungiyar Turai Federica Mogherini a daren jiya Talata, Wakilin Musaman na MDD kan Kasar Siriya Stefen De Mustura ya ce a wannan Laraba kwamitin tsaron MDD zai yi zaman gaggauwa dangane da harin makami mai guba da aka kai Siriya.
Har ila yau De Mustura ya kara da cewa MDD za ta ci gaba da kokari ta sahihiyar hanya wajen magance rikicin kasar Siriya,shakka babu irin zaman da Duniya ke yi a gariruwan Ganeva da kuma Brussel shi ke kara nuna irin kokarin da ake yi na kokarin magance rikicin kasar Siriya ta sahihiyar hanya.
De Mustura ya ce duk lokacin da MDD ke kokarin daukan wani mataki na magance rikicin kasar Siriya sai ta fuskanci matsin lamba daga wasu manyan kasashe na Duniya.