WHO : An Samu Ci Gaba A Yaki Da Zazzabin Cizon Sauro
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19778-who_an_samu_ci_gaba_a_yaki_da_zazzabin_cizon_sauro
Hukumar lafiya ta MDD, ta ce an samu ci gaba da ci gaba matuka a yaki da cutar zazzabin cizon sauro a fadin duniya inda tsakanin shekara 2010 zuwa 2015 aka samu raguwar ciwan da kashi 21%.
(last modified 2018-08-22T11:30:01+00:00 )
Apr 25, 2017 05:42 UTC
  • WHO : An Samu Ci Gaba A Yaki Da Zazzabin Cizon Sauro

Hukumar lafiya ta MDD, ta ce an samu ci gaba da ci gaba matuka a yaki da cutar zazzabin cizon sauro a fadin duniya inda tsakanin shekara 2010 zuwa 2015 aka samu raguwar ciwan da kashi 21%.

A cewar rahoton na WHO an samu ragowar mace-mace sanadin ciwan na Maleria da kashi 29% a cikin tsawan shekaru biyar da suka wuce.

A yankin kudu da hamadar sahara na Afrika barazanar ciwan zazzabin cizan sauron ya ragu da kashi 21% har zuwa 31%.

Hukumar ta ce kasashe da dama sunyi iyakacin kokari wajen yaki da zazzabin na Maleria, amman duk da hakan ciwan na zama babban kalubale ga sha'anin kiwan lafiyar al'umma, don haka ya zama wajibi a kara zage damtse.

A shekara 2015 data gabata cutar zazzabin Maleria ta kashe mutane 429,000 a fadin duniya, sanan wani binkice ya nuna cewa cutar na yin sanadin mutuwar yaro guda a cikin ko wanne dakikoki biyu.

A hakin da ake ciki dai Hukumar ta (WHO) ta ce za ta fara gwajin rigakafin cutar a kasashe 3 na Afirka da suka hada da Ghana, Kenya da kuma Malawi.

Yau 25 ga watan Afrilu ita ce dai ranar da MDD ta ware domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro.