ICC Ta Fitar Da Sammacin Kame Tsohon Shugaban Tsaron Ghaddafi
Kotun hukunta mayan laifuka ta duniya wato (ICC) ta fitar da sammacin kame mata tsohon shugaban hukumar tsaron mirigayi Mu'ammar Ghaddafi na Libya.
ICC dai na tuhumar Al-Touhami Khaled da laifukan yaki da kuma cin zarafin bil adama a lokacin guguwar neman sauyi ta al'ummar kasar a cikin shekara 2011.
Sammacin na shekara 2013 wanda a yanzu ne aka fitar da shi ya kuma zargi wasu mayan jami'an tsaro hudu da laifukan cin zarafin bil adama tsarewa a gidan kurkuku, fyade muzgunawa da dai sauren wasu laifuka makamantansu na kuntatawa dan adam.
Duk dai laifukan a cewar kotun ta ICC an aikata su ne tsakanin watan Fabariru da kuma Agusta na shekara 2011, domin kawo karshen masu boren nuna adawa da gwamnatin mulkin Ghaddafi ta ko wanne irin hali.
A watan Afrilu na 2012 an dai cafke Al-Touhami Khaled a kasar Masar sai dai daga bisani aka sallame shi kasancewar ba'a fitar da sammacin kame shi ba, kuma tun lokacin aka daina jin duriyarsa.