Matakin Amurka Na Tsoma Baki A Harkokin Kasashen Iraki Da Siriya
Shugaban kasar Amurka ya bai wa sakataren tsaron kasar damar tantance yawan sojojin Amurka da za a tura kasashen Iraki da Siriya da sunan yaki da ta'addanci.
Jaridar The Hill ta kasar Amurka a jiya Laraba ta watsa labarin cewa: Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bai wa sakataren tsaron kasar James Mattis cikakkiyar damar tantance yawan sojojin Amurka da za a tura zuwa kasashen Iraki da Siriya da sunan yaki da ta'addanci.
Wannan mataki da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na bai wa hukumar tsaro ta Pentagon damar tantance yawan sojojin Amurka da za a tura zuwa kasashen Iraki da Siriya yana zuwa ne a daidai lokacin da al'ummun kasashen na Iraki da Siriya suke ci gaba da kokawa kan yadda sojojin Amurka suke daukan matakan wuce gona da iri kansu.