An Bude Babban Baje Kolin Tufafin Mata Musulmi A Indonesia
A yau ne aka bude babban baje kolin tufafin mata na musulunci a kasar Indonesia tare da halartar kamfanoni na kasashen ketare.
Shafin yada labarai na Netral News ya habarta cewa, an bude baje kolin ne a tsibirin Jawa na kasar Indonesia, tare da halartar wakilan kamfanoni da ke samar da tufafin musulunci na mata, da suka hada da dogayen riguna da kuma hijabai da mayafan kai da sauransu.
Wannan baje koli na kasa da kasa na tufafin muslunci zai dauki tsawon kwanaki hudu a jere ana gudanar da shi, yayin da kamfanonin dinka tufafin mata na cikin gida daga dukkanin sassa na kasar ta Indonesia suka nuna samfur-samfur na kayayyakin da suke samarwa.
Samar da tufafi na daga cikin uhimman hanyoyi na samun kudaden shiga ga kasar ta Indonesia, inda akan fitar da kayayyaki da suka danganci tufafi da sukan kai na biliyoyin daloli a kowace shekara zuwa kasashen ketare.
Kasar Indonesia dai ita ce kasar musulmi da tafi yawan jama'a, inda fie da kashi 90 cikin dari na mutanen kasar da yawansu ya haura miliyan 242 mabiya addinin muslunci ne.