Faransa : Macron Zai Ziyarci Sojojin Kasarsa A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20492-faransa_macron_zai_ziyarci_sojojin_kasarsa_a_mali
A gobe Juma'a ne ake sa ran shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron zai ziyarci sojojin kasarsa dake jibge a kasar Mali.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
May 18, 2017 15:11 UTC
  • Faransa : Macron Zai Ziyarci Sojojin Kasarsa A Mali

A gobe Juma'a ne ake sa ran shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron zai ziyarci sojojin kasarsa dake jibge a kasar Mali.

Wannan Ziyarar dai za ta kasance ta farko da Mista Macron zai kai zuwa nahiyar Afirka a matsayin shugaban kasar ta faransa. 

Mista Maccon zai ziyarci sansanin sojojin faransa dake yankin Gao inda zai gana dasu domin jinjina masu.

A shekara 2012 yankin arewacin Mali ya fada hannun mayakan jihadi dake da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta Al Qaïda sanadin rikicin yan tawayen buzaye, lamarin daya cilasta aikewa da dakarun kasa da kasa bisa bukatar kasar Faransa domin yakar mayakan masu kaifin kishin addini.

Tawagar mai suna Barkhane dai ta kunshi sojoji 4,000 da aka baza a wasu kasashen yankin Sahel 5 da suka hada da Mali, Burkina-Faso, Mauritania, Nijer da kuma Chadi.

Ko a watan Janairu na wannan shekara tsohon shugaban faransar, Faransoi Hollande ya ziyarci tawagar sojojin kasar tasa da kuma na Mali a yankin na Gao.