Shugaban Sudan Ya Janye Aniyarsa Ta Halartar Taron Saudiyya Da Trump
(last modified Fri, 19 May 2017 17:53:01 GMT )
May 19, 2017 17:53 UTC
  • Shugaban Sudan Ya Janye Aniyarsa Ta Halartar Taron Saudiyya Da Trump

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan al-Bashir ya sanar da janyewarsa daga gayyatar da sarkin Saudiyya yayi masa na ya halarci kasar don ganawa da shugaban kasar Amurka Donald Trump wanda zai fara ziyarar aiki a kasar Saudiyya a gobe Asabar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Sudan din SUNA ne ya bayyana hakan inda ya ce saboda wasu dalilai masu muhimmanci, shugaba Bashir din ba zai sami damar halartar taron ba. Sanarwar dai ba ta fadi wadannan dalilan ba, to amma ta kara da cewa tuni shugaba Bashir din ya aike wa sarkin Saudiyya Salman sakon neman uzurin rashin halartar taron, sai dai kuma babban daraktan ofishinsa Taha Al-Hussein zai wakilce shi a wajen taro.

A kwanakin baya ne dai sarkin Salman din ya aike wa wasu shugabanni da firayi ministocin kasashen musulmi ciki kuwa har da shugaba Al-Bashir din goron gayyatar halartar wannan taron da za a gudanar a birnin Riyadh a ranar Lahadi mai zuwa tare da shugaban Amurka.

Tun da fari dai gayyatar shugaba al-Bashir din da sarkin Saudiyyan yayi ya janyo hankula bisa la'akari da ci gaba da nemansa ruwa a jallo da kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffukan yaki ta ke yi saboda zargin aikata laifukan yaki a rikicin Darfur na kasar inda dubun dubatan  mutane suka mutu.