An Bukaci Kawo Karshen Yakin Cikin Gida A Kasar Libya
Kasashen da suke makobtaka da kasar Libya sun bukaci taimakon kungiyar kasashe 7 mafi karfin tattalin arziki a duniya da su taimaka wajen kawo karshen rikicin cikin gida na kasar Libya.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto shugaban kasar Niger Mohammadu Yusuf yana fadar haka a taron G7 wanda aka kammala a kasar Italia a jiya Asabar. Yusuf ya kara da cewa yaki da ta'addanci a arewacin Afrika ba tare da kawo karshen rikicin cikin gida na kasar Libya ba ba zai taba yiyuwa ba.
Shugaban kasar ta Niger ya bukaci kasashen G7 da MDD da kuma tarayyar Turai da su tallafawa kasashen yankin Sahel 5, da kayan aiki don ganin sun samar da rundunar kasa da kasa wacce zata dawo da zaman lafiya a kasar ta Libya.
Banda haka shuwagabannin kungiyar ta G7, da MDD da kuma tarayyar Turai su ma sun yi kira ga shuwagabannin siyasa a kasar Libya da su mutunta yerjejeniyar zaman lafiya da suka kulla a tsakaninsu don kawo kasar zabar da jini a kasar, amma basu bayyana cewa ko zasu shiga kai tsaye don tabbatar da hakan ba.