Jun 15, 2017 23:03 UTC
  • Putin: Muna Da Shirin Kara Karfafa Rundunar Sojin Syria Da Makamai Na Zamani

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, Rasha tana da shirin karfafa rundunar sojin kasar Syria da wadatattun makamai na zamani.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, shugaba Putin ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, a wani shirinsa na shekara-shekara, inda yakan karba wayoyin tarho kai tsaye na mutanen kasar Rasha a gidan talabijin, domin jin korafe-korafen jama'a da kuma amsa tambayoyinsu a kan batutuwa da suka shafi gwamnati da ayyukanta.

A lokacin da yake magana a kan batun Syria da kuma mara baya da gwamnatin Rasha ke yi ga Syria wajen yaki da 'yan ta'adda, Putin ya bayyana cewa gwamnatinsa na da shirin bayar da wasu makamai na zamani ga rundunar sojin Syria, domin murkushe 'yan ta'adda, domin al'ummar Syria su rayu cikin aminci da zaman lafiya kamar sauran al'ummomi na duniya.

Tags