MDD Ta Bukaci Magance Rikicin Djibouti Da Eritrea Ta Hanyar Shawarwari
Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya, ya bukaci kasashen Djibuti da Eritrea da su magance rikicin Iyakokinsu ta hanyar shawarwari.
A taron daya gudanar jiya Litini kwamitin ya bukaci bangarorin biyu da su magance wannan sabanin ta hanyar lumana kamar yadda dokokin kasa da kasa suka shata.
Kasashen 15 mamboboi kwamitin sun kuma yaba da shawarar da kungiyar tarayya Afrika ta bayar na tura tawagar soji a iyakar kasashen.
Kasar Habasha ce dai ta bukaci taron kwamitin na tsaro kan rikicin iyakar da ya kunno kai tsakanin kasashen biyu bayan ficewar sojojin kasar Qatar daga yankin.
Kafin hakan dai Kasar Djibuti ta zargi makofciyarta Eritrea, da amfani da ficewar sojojin na Qatar domin mamaye wani bangare na yankin da kasashen biyu na yankin kahon Afrika ke takkadama a kai.
A 'yan kwanakin nan ne Qatar ta sanar da janye sojojinta daga yankin biyo bayan Djibouti ta dauki matakin mara wa Saudiyya baya a rikicin diflomatsiya na tsakanin Qatar da kasashen na tekun Pasha.