Jul 10, 2017 06:18 UTC
  • Limamai A Turai Na Jerin Gwanon Kyammar Ta'addanci

Wasu jagororin al'ummar musulmin turai sun hallara a wani gangami na kyammar ayyukan ta'addanci a birnin Balin na Jamus domin nunawa duniya yadda addinin na Islama ba shi da wata alaka da ta'addaci.

A birnin na Balin masu ganganmin sun ziyarci kasuwar nan ta saida kayan Kirsimeti inda wani hari da babbar mota ya kashe mutane 12 a watan Disamban bara, inda suka gudanar da addu'o'i.

A faransa ne dai aka kaddamar da wannan jerin gwanon, kuma za'a kammala shi a kasar data kunshi mafi yawan al'ummar musulmi a nahiyar Turai, a ranar 14 ga watan nan na Yili da muke ciki.

Masu gangamin dai na samun rakiyar wakilan sauren addinai na yankin da suka hada da Kristoci da kuma Yahudu.

Kafin hakan dai limanin birnin Lisbonne, David Munir, ya bayyana a birnin Paris cewa wannan shi ne irinsa na farko a turai, kuma babbar manufarsa ita ce  isar da sako ga duniya na cewa musulinci addinin zamen lafiya ne, wanda baida wata alaka da abubuwan dake faruwa na ta'addanci.

Tags