WHO : Ana Bukatar Dala Biliyan 274 Don Inganta Harkokin Lafiya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i22344-who_ana_bukatar_dala_biliyan_274_don_inganta_harkokin_lafiya
Mujallar kiwon lafiya ta The Lancet Global Health, ta ce ana bukatar a kalla dala biliyan 274 a kowacce shekara, domin cimma muradun kiwon lafiya na MDD a kasashen masu karanci da matsakaicin kudin shiga.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jul 18, 2017 06:33 UTC
  • WHO : Ana Bukatar Dala Biliyan 274 Don Inganta Harkokin Lafiya

Mujallar kiwon lafiya ta The Lancet Global Health, ta ce ana bukatar a kalla dala biliyan 274 a kowacce shekara, domin cimma muradun kiwon lafiya na MDD a kasashen masu karanci da matsakaicin kudin shiga.

Wadanda kasashen a su kadai sun mamaye kashi 75% na al'ummar duniya.

Binciken na baya baya nan da aka aiwatar wanda Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta dauki nauyi, shi ne ya yi kiyasin kudaden da za a kashe da kuma moriyar da za a samu na fadada harkokin kiwon lafiya, domin cimma muradun ci gaba masu dorewa 16 na kiwon lafiya a kasashen 67.

Ayyukan za su kare mace-macen kuruciya da kusan miliyan 97 a duniya daga yanzu zuwa shekarar 2030.