Hanyar Kalubalantar Matsalar Kwararan Bakin Haure Zuwa Kasashen Yammacin Turai
A kokarin da ake yi na shawo kan matsalar kwararan bakin haure zuwa kasashen yammacin Turai, wakilan kasashen Turai da na Afrika 10 gami da wasu kungiyoyi 4 masu zaman kansu sun cimma yarjejeniya kan bin hanyoyin da suka dace domin kalubalantar matsalar kwararan bakin hauren zuwa kasashen Turai musamman ta hanyar teku.
Jaridar Al-Shuruq ta kasar Tunusiya ta habarta cewa: Wakilan kasashe goma daga nahiyar Yammacin Turai da Afrika sun gudanar da wani zaman taro a kasar Tunusiya a farkon wannan mako da nufin neman hanyoyin da suka dace su bi wajen kalubalantar matsalar kwararan bakin haure zuwa kasashen yammacin Turai musamman ta hanyar tekun Mediterrenea.
Mahalatta zaman taron sun tattauna batun karfafa taimakekkeniya a tsakaninsu musamman musayar bayanan sirri kan hanyoyin dakile masifar kwararan bakin haure zuwa kasashen yammacin Turai ta hanyar teku lamarin da ke kai ga halakar rayukan bil-Adama masu yawa a kullum rana.
Wakilan kasashen da suka halacci zaman taron sune; Libiya, Aljeriya, Faransa, Italiya, Malta, Jamus, Chadi, Niger, Mali da Tunusiya baya ga wasu kungiyoyi masu zaman kansu. A jawabinsa a zaman taron ministan harkokin cikin gidan kasar Tunusiya Hadi Majdub ya bayyana cewa; Dukkanin mahalatta zaman taron sun kai ga tabbacin cewa babu wata kasa ita kadai da zata iya magance matsalar bakin haure ba tare da samun hadin kai da tallafin sauran kasashe ba.
A cikin 'yan shekarun baya-bayan nan kasashen Afrika da dama da bakin hauren suke amfani da gabar tekunsu wajen shirya tafiya zuwa kasashen yammacin Turai ta hanyar teku, sun matsa kaimi a fagen dakile irin wannan tafiye-tafiye amma lamarin ya cutura sakamakon tarin matsalolin da suke zaburar da bakin hauren musamman matsalolin siyasar kasashensu, yakin basasa, habakar ayyukan ta'addanci, rashin tsaro, talauci da sauransu.
Bincike yana nuni da cewa: Dukkanin tsauraren matakai da aka dauka a baya da nufin dakile kwararan bakin haure zuwa kasashen Yammacin Turai ta hanyar teku sun gaza cimma nasara sakamakon tarin matsalolin da suke zaburar da bakin hauren daga kasashensu lamarin da a halin yanzu ya tilastawa manyan kasashen yammacin Turai fara tunanin neman hanyar rage tarin matsalolin da suke addabar kasashen da bakin hauren suke fitowa da nufin ganin an samu saukin masifar kwararansu zuwa kasashen na Turai.