Aug 23, 2017 05:25 UTC
  • 'Yan Buddha Sun Kaddamar Da Wasu Sabbin Shirye-Shiryen Takura Wa Musulmin Myammar

Rahotanni daga kasar Myammar sun bayyana cewa mabiya addinin Buddha masu tsaurin ra'ayi sun kara killace wasu daruruwan musulmi Rohingya a jihar Rakhine a ci gaba da takura musu da suke yi.

Rahotannin sun jiyo al'ummomin kauyen Zay Di Pyin da ke jihar Rakhine din suna fadin cewa kimanin musulmi 700 ne 'yan Buddha suka killace su da hana su fita zuwa aiki ko zuwa kasuwa don sayen abubuwan da suke bukata bugu da kari kan hana su ruwan sha.

Kungiyoyi masu sanya ido da kuma kai agaji na kasa da kasa da suke kasar ta Myammar dai sun tabbatar da wannan labarin inda suka ce masu tsaurin ra'ayin sun killace musulmi a yankin ta yadda ba su da wata hanya ta samun abubuwan da suke bukata na rayuwar yau da kullum.

Wannan yanayin dai shi ne zalunci na baya-bayan nan da 'yan Budha masu tsaurin ra'ayi da suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Myammar din suke yi wa musulmin Rohingya din wadanda sun kai mutane miliyan guda suke rayuwa a yankunan arewacin kasar.

 

 

Tags