MDD: Yanayin Kasar Libiya Lamari Ne Mai Tada Hankali Ainun
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tsananin damuwarta dangane da yanayin da kasar Libiya ta ke ciki duk kuwa da kokarin da kasashen makwabta suke yi wajen kyautata yanayin tsaro a kasar.
A yayin da yake bayanin hakan a zaman da Kwamitin Tsaron MDD yayi ya gudanar a daren jiya don dubi kan yanayin kasar Libiyan, manzon MDD na kan kasar Libiya Ghassan Salamé ya ce duk da kokarin da kasashen da suke makwabtaka da Libiyan suke yi, to amma yanayin tattalin arziki da zamantakewar kasar lamari ne mai tada hankali.
Mr. Salame ya kara da cewa raunin da cibiyoyin gwamnati suka yi da gazawarsu wajen aiwatar da ayyukan da ya dace lamari ne da ke kara munin da kasar Libiyan take ciki, kamar yadda kuma ya ce 'yan gudun hijira da sauran bakin haure da suke shigowa kasar lamari ne da ke kara munin yanayi a kasar, don haka yayi kiran dukkanin bangarorin da lamarin Libiya ya shafa da su yi wata hobbasa wajen ceto kasar.
Tun dai bayan da aka kifar da tsohuwar gwamnatin marigayi Kanar Gaddafi a shekara ta 2011 kasar Libiya ta shiga cikin mawuyacin hali na tsaron, tattalin arziki da zamantakwa.