Jamus Ta Bayyana Taimakon Da Take Bayarwa Na Bunkasar Kasashen Afirka
Shugabar gwamnatin Jamus ta tabbatar da taimakon da take bayar wa na bunkasar kasashen Afirka da nufin magance matsalar kwararar bakin haure zuwa kasashen Turai.
A yayin da take jawabi a taron shugabanin kasashen Afirka da Turai kan matsalar bakin haure, Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tabbatar da yakar tushen masu safarar mutane, tare da bayyana cewa kasar Jamus za ta halarci duk wani shiri na bunkasar kasashen turai da Afirka.
Wannan firici na shugaban gwamnatin jamus na zuwa ne a yayin da matsalar kwararar baki haure cikin 'yan shekarun nan ya zamewa kasashen Turai wata babbar matsala dake cima magabatan kasashen tuwo a kwarya. duk da cewa an dauki wasu matakai da suka rage kwararen bakin haure daga wasu yankuna na gabas ta tsakiya, to amma har yanzu ana ci gaba da fuskantar wannan matsala a Afirka, ganin halin da kasar Libiya ke ciki, masu safarar mutane na amfani da wannan dama wajen safarar mutane zuwa kasashen Turai, inda mutane da dama ke rasa rayukansu a kan hanya kafin shiga cikin kasashen turan.
Matsalar tattalin arziki, talauci da rashin aikin yi, yaki da rikicin cikin gida, wanda hakan ke janyo rashin konciyar hanakali da tsaro, na daga cikin mahiman dalilan da suke sanya wasu 'yan kasar Afirka yin hijra zuwa turai, a yayin da shugabanin na turai ke riyar cewa suna bayar da taimako a bunkasar tattalin arzikin kasashen Afirka.
Wannan maudu'i ana iya kallonsa ta mahanga daban daban daga ciki kuwa shi ne, Kasashen yamma musaman ma na turai su ne sanadiyar halin da kasashen Afirka suka ciki a yau, domin da dama daga cikin kasashe Afirka sun kasance cikin kangin milkin mallaka na wadannan kasashe, tushe duk wasu hanyoyi na ci gaba a bangaren tattalin arziki,siyasa da zamantakewa, sanya sabani a tsakanin kabilu da sabanin addini, domin kwashe albarkatun karkashin kasa na kasashen Afirka, kirkiro 'yan tawaye ga gwamnatin da bata tafiya a kan manufofinsu tare da goyon bayansu, na daga cikin mumunar siyasar Turai da take gudanarwa a kasashen Afirka,matsalar kasar Libiya na a matsayin misali game da hakan, kuma a halin da ake cikin kasar Libiyan ta zamanto wata hanya na kwararar bakin haure zuwa kasashen Turai.
A cewar Luisa Morgantini tsohuwar mataimakiyar shugaban majalisar Turai, lallai wajibi ne a kula da matsalar kwararar bakin haure zuwa kasashen Turai, to amma ya kamata a fahimci cewa masu neman mafuka zuwa kasashen turan na yin hakan ne sanadiyar yaki da rashin tsaro da ya samo asali daga siyasar kasashen Amurka da Turai a gabas ta tsakiya da arewacin Afirka.
A bangare guda, yayin da wadannan kasashe ke riyar bayar da taimakon bunkasar kasashen Afirka, a gefe guda kuma suna ci gaba da siyasar su ta yin kacal a harakokin cikin gidan kasashen na Afirka, kuma ba sa bayar da taimako haka nan , ba tare da sun gindaya sharadi ba,wanda amfanin hakan na komawa ne zuwa kasashensu, daga ciki kuwa taimakon da za su bayar bisa sharadin cewa duk kasar da za ta karbi wannan taimako ya zama wajibi ta dauki matakin dakatar da hana mutanan dake son zuwa kasashen turai bi ta cikin kasar ta.
A halin da ake ciki, kasashen Turai sun kebe wani taimako da za bayar ga wasu kasashen Afirka domin magance matsalolinsu na hana kwararan bakin haure, to amma ita kuma matsalar kasashen Afirka za ta ci gaba da zama a inda take ko ma ta karu, sanadiyar wannan mataki na hana kwararan bakin haure zuwa kasashen na turai.