MSF Ta Kalubalanci Yadda Ake Gallazawa Bakin Haure A Libiya
Kungiyar likitoci ta kasa da kasa ta bayyana damuwarta akan yadda ake gallazawa bakin hauren dake kokarin shiga turai ta tekun Bahar Rum.
kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata wasika data aikewa gwamnatocin kasashen turai, wanda ta ce suke nuna halin ko in kula akan yadda ake muzgunawa bakin hauren.
Shugabar Kungiyar ta MSF, Joanne Liu, ta bayyana a wasikar cewa kasashen turan su ne silan gallazawar da akewa bakin hauren, don kuwa manufarsu guda ce kawai a hana bakin hauren kwararen zuwa kasashensu ta ko wanne hali.
Madame Liu, ta bayyana hakan ne bayan ziyarar data kai a wata cibiya da ake tsare bakin hauren a kasar Libiya, inda ta koka matuka kan irin yanayin data samu bakin hauren dake jibge a wurin da bai dace da rayuwar dan adam ba.