Yan Gudun Hijiran Somalia A Yemen Suna Barin Kasar Saboda Yaki
MDD ta bada sanarwan cewa yan gudun hijirar kasar Somalia wadanda suka gudu daga kasarsu a shekarun baya zuwa kasar yemen a halin yanzu suna kaura daga kasar sanadiyyar yaki da kuma barazanar fari.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto kakakin hukuma mai kula da yan gudun hijira na MDD a kasar Yemen Shabia Mantoo tana fadar haka a yau Alhamis .Ta kuma kara da cewa a cikin makonni ukku da suka gabata yan gudun hijira daga kasar Somalia 284 suka koma kasarsu .
Mantoo ta kara da cewa hukumarta, da na wata kungiya mai zaman kanta ne suka dauki hayar jiragen ruwa biyu a birnin Adan na kasar ta Yemen wadanda suka yi jiglar yan gudun hijiran zuwa tashar jiragen ruwa na Berbera a kasar Somalia.
MDD ta bayyana cewa daga farkon wannan shekara zuwa watan Afrilu yan gudun hijira daga Somalia dubu 55 suka isa kasar Yemen duk tare da yakin da take ciki da kuma kellacewar da kasar saudia takewa kasar.
Hakama kungiyar Red Cross ta bayyana cewa tun farkon wannan shekara zuwa watan Afrilu mutane 2,100 suka mutu sanadiyyar yaki daga cikin yan gudun hijirar kasar ta Somalia a Yemen