MDD : Saudiyya Na Kisan Yara A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/world-i24683-mdd_saudiyya_na_kisan_yara_a_yemen
A karon farko Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kawancen da Saudiyya ke jagoranta a Yemen da kisa da kuma gallazawa yara.
(last modified 2018-08-22T11:30:47+00:00 )
Oct 06, 2017 08:58 UTC
  • MDD : Saudiyya Na Kisan Yara A Yemen

A karon farko Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kawancen da Saudiyya ke jagoranta a Yemen da kisa da kuma gallazawa yara.

Wannan dai na kunshe ne a rahoton shekara-shekara da babban sakatare na MDD ke fitarwa kan cin zarafin yara a duniya.

Babban sakatare na MDD Antonio Guterres ya bayyana a cikin rahoton cewa sama da yara 8,000 ne suka gamu da ajalisu ko kuma aka lahanta a hare-haren wuce gona da iri da aka kai a cikin shekara 2016.

Makasudin fitar da irin wannan rahoto a ko wacce shekara a cewar Mista Guteress, shi ne kawo karshen miyagun halayen da suka hada da kisa, nakasawa, cin zarafi, fyade, garkuwa da dai saurensu da akewa yara a lokutan yake yake a duniya.