Kofi Anan: Matasa Ba Su Makara Ba Wajen Jagorantar Al'ummominsu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i24759-kofi_anan_matasa_ba_su_makara_ba_wajen_jagorantar_al'ummominsu
Tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya kirayi matasa da su mike wajen sauke nauyin da ke wuyansu dangane da al'ummominsu yana mai cewa matasan ba su makara ba wajen jagorantar al'ummomin na su.
(last modified 2018-08-22T07:00:48+00:00 )
Oct 08, 2017 13:34 UTC
  • Kofi Anan: Matasa Ba Su Makara Ba Wajen Jagorantar Al'ummominsu

Tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya kirayi matasa da su mike wajen sauke nauyin da ke wuyansu dangane da al'ummominsu yana mai cewa matasan ba su makara ba wajen jagorantar al'ummomin na su.

Mr. Kofi Annan ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar wajen taron kasa da kasa na matasa da aka gudanar a garin Bogota na kasar Kolombiya inda ya ce maganar cewa matasa ba za su iya rike mukamai masu muhimmanci ba bai ma taso ba, yana mai cewa matasa suna iya taka gagarumar rawa a wannan bangaren musamman a irin wannan duniya da muke ciki.

Tsohon babban sakataren MDD ya bayyana wa matasan cewa lalle ina sake jaddada muku cewa ba ku yi gaggawa ba idan har kuka ce za ku yi jagoranci. A saboda haka ya ce yana kiran matasan da su ba da himma kana kuma su yi amfani da karfin da Allah yayi musu wajen ciyar da al'ummominsu gaba da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma.

Taron dai ya sami halartar manyan baki daga kasashe daban-daban da suka hada da shugaban kasar Kolombiyan, Juan Manuel Santos da sananniyar mai kare hakkokin bil'adaman na kasar Afirka ta Kudu, Thuli Madonsela da dai sauransu.