MDD: Yanayin Da Al’ummar Yemen Suke Ciki Mai Daga Hankali Ne
https://parstoday.ir/ha/news/world-i25215-mdd_yanayin_da_al’ummar_yemen_suke_ciki_mai_daga_hankali_ne
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar yanayin bil’adama a kasar Yemen, wacce take karkashin hare-haren wuce gona da iri na kasar Saudiyya da kawayenta na sama da shekaru biyu da rabi, wani yanayi ne mai tada hankalin gaske.
(last modified 2018-08-22T07:00:54+00:00 )
Oct 28, 2017 14:30 UTC
  • MDD: Yanayin Da Al’ummar Yemen Suke Ciki Mai Daga Hankali Ne

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar yanayin bil’adama a kasar Yemen, wacce take karkashin hare-haren wuce gona da iri na kasar Saudiyya da kawayenta na sama da shekaru biyu da rabi, wani yanayi ne mai tada hankalin gaske.

Shugaban Hukumar ba da agaji na gaggawa na Majalisar Dinkin Duniyan Mark Lowcock ne ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai jim kadan bayan gama wani ran gadi na kwanaki biyar da ya kai kasar Yemen din inda ya ce ya zama wajibi a kawo karshen wannan yaki ta hanyar tattaunawa ta siyasa.

Mr. Lowcock ya ce ya zo kasar Yemen din don gane wa idanuwansa halin da ake ciki a kasar Yemen din musamman irin yadda cutar Kwalara take ci gaba da yaduwa a kasar wanda ba a taba ganin irinsa ba a duniya, don haka ya kirayi dukkanin bangarorin da suke cikin rikicin da su zauna a teburin tattaunawa don kawo karshen rikicin.

Tun a watan Maris din shekara ta 2015 ne dai kasar Saudiyya ta jagoranci wasu kawayenta wajen kaddamar da hare-hare kan al’ummar Yemen din ta hanyar fakewa da batun dawo da tsohon shugaban kasar Abdurrab Hadi Mansur lamarin da ya zuwa yanzu yayi sanadiyyar sama da mutane 12,000 baya ga wasu dubban da suka samu raunuka.