Kasashen Afirka Na Bukatar Kujeru Biyu A Kwamitin Tsaro Na MDD
(last modified Sun, 12 Nov 2017 05:52:09 GMT )
Nov 12, 2017 05:52 UTC
  • Kasashen Afirka Na Bukatar Kujeru Biyu A Kwamitin Tsaro Na MDD

Wakilin kasar Aljeriya a MDD Mohammed BESSEDIK ya bukaci a gudanar da canji tare da bawa kasashen Afirka kujeru biyu na din din din a kwatinin tsaro na MDD.

Kamfanin dillancin labaran Waaj na kasar Aljeriya ya nakalto Mohammed BESSEDIK daga birnin New York a wannan Asabar na cewa a kwai bukatar  yiwa kwamitin tsaron MDD canji musamman game da manbobin kwamitin idan aka yi la'akari da alakar dake tsakanin Kwamitin da MDD da kuma batun hakin beto.

Wakilin kasar Aljeriyan a MDD ya kara da cewa ba abin da za a amince da shi ba ne a ce  kasashen Afirka ba  su da kujerar din din din a kwamitin tsaron MDD ba, wannan yanayi ba zai ci gaba da zama a haka ba.

Bessedik ya kara da cewa kamata yayi kwamitin tsaron MDD ya kasance cikin tsarin demokaradiya domin ya iya tasiri sosai a idanun al'ummar duniya.

Kwamitin tsaron MDD nada manbobi guda biyar masu kujerar din- din- din  da kuma mambobi goma da ake zabe, manbobi biyar na farko (wato su ne wakilan kasashen Amurka, Birtaniya, Rasha, China da Faransa) suke da hakkin daukan kuduri a kwamitin.