Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Kawo Karshen Killace Kasar Yamen
https://parstoday.ir/ha/news/world-i25454-majalisar_dinkin_duniya_ta_bukaci_kawo_karshen_killace_kasar_yamen
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kawo karshen killace Yamen da rundunar kawancen Saudiyya take yi wa kasar ta sama da ruwa da kuma ta kasa.
(last modified 2018-08-22T11:30:59+00:00 )
Nov 14, 2017 06:18 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Kawo Karshen Killace Kasar Yamen

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kawo karshen killace Yamen da rundunar kawancen Saudiyya take yi wa kasar ta sama da ruwa da kuma ta kasa.

Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric a jiya Litinin ya jaddada cewa: Al'ummar Yamen suna cikin halin tsaka mai wuya sakamakon killace kasarsu da rundunar kawancen Saudiyya ta yi ta sama da ruwa da kuma kasa lamarin da ya hana shigar da kayayyakin jin kai cikin kasar.

Dujarric ya kara da cewa: Al'ummar Yamen suna tsananin bukatar tallafin gaggawa musamman kayayyakin abinci, makamashi da kuma magunguna.

Har ila yau wakiliyar Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" a kasar ta Yamen Meritxell Relano a ranar Juma'ar da ta gabata ta yi furuci da cewa: Al'ummar Yamen suna suna cikin mawuyacin hali, inda akwai miliyoyin mutane da suke bukatar tallafin gaggawa a kasar.