An Cimma Sakamako Mai Kyawo A Taron Sauyin Yanayi Na Bonn
(last modified Sun, 19 Nov 2017 10:24:01 GMT )
Nov 19, 2017 10:24 UTC
  • An Cimma Sakamako Mai Kyawo A Taron Sauyin Yanayi Na Bonn

Shawarwarin da aka yi a tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa, a taro kan sauyin yanayi na Bonn an cimma sakamako mai kyau a yayin taron

Bisa shawarwarin da aka yi a tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa, an cimma sakamako mai kyau a yayin taron, lamarin da zai ba da gudummawa sosai wajen kammala shawarwari kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar Paris a kan lokaci.

Cikin wannan taron da aka yi a birnin Bonn na tarayyar Jamus, an zartas da kudurori da dama da suka hada da shirin gudanarwa ta Fiji da dai sauransu. Haka kuma, an tsara wani daftarin yin shawarwari mai kiyaye daidaituwa a tsakanin bangarori daban daban wanda Yarjajeniyar Paris ta shafa, inda aka tabbatar da matsaya kan yadda za a gudanar da taron shawarwari na shekarar 2018, yayin tsara jadawalin gaggauta ayyukan kiyaye yanayin duniya kafin shekarar 2020.