Nov 24, 2017 05:15 UTC
  • AU Ta Zargi Kasashen Turai Da Hannu Cikin Matsalar 'Yan Gudun Hijira Na Afirka

Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka kuma shugaban kasar Guinea Conakry, Alpha Konde, ya bayyana cewar kasashen Turai suna da hannu cikin wani bangare na matsalolin da 'yan gudun hijira daga Afirka suke fuskanta a kasar Libiya.

Shugaba Alpha Konde ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai da yayi tare da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron inda ya ce kasashen Turai sun taimaka cikin matsanancin halin da 'yan gudun hijiran Afirka suke fuskanta a halin yanzu a kasar Libiya don kuwa a cewarsa kasar Libiyan ba ta da karfin da ake bukata wajen kula da 'yan gudun hijirar.

Shugaban yana mayar da martani ne ga wani rahoto da ke cewa kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta bukaci gwamnatin Libiyan da ta hana 'yan gudun hijira Afirkawan daga shiga Turai din matukar kasar tana son ta taimaka mata da kudade.

Cikin makon da ya wuce ne dai wasu kafafen watsa labarai suka ba da labarin yadda ake sayar da 'yan gudun hijira da suka shigo kasar Libiyan daga kasashen Afirka daban-daban da suke son tafiyar Turai din a matsayin bayi bisa farashin kudin da bai taka kara ya karya ba. Wasu rahotannin sun ce ana sayar da su din ne a kan kudi Dalar Amurka 400 lamarin da ya fuskanci tofin Allah tsine daga gwamnatocin yanki da kuma wasu kungiyoyi na kasa da kasa.

Tags