Rahoton MDD Kan Ci Gaba Da Kisan Fararen Hula A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/world-i26499-rahoton_mdd_kan_ci_gaba_da_kisan_fararen_hula_a_yemen
Kakakin Hukuma Kare hakin bil-adama ta MDD ya sanar da cewa harin wuce gona da iri da kawancen saudiya ke kaiwa kasar Yemen yayin sanadiyar mutuwar fararen hula 136.
(last modified 2018-08-22T11:31:10+00:00 )
Dec 19, 2017 18:58 UTC
  • Rahoton MDD Kan Ci Gaba Da Kisan Fararen Hula A Yemen

Kakakin Hukuma Kare hakin bil-adama ta MDD ya sanar da cewa harin wuce gona da iri da kawancen saudiya ke kaiwa kasar Yemen yayin sanadiyar mutuwar fararen hula 136.

Kamfanin dillancin labaran Fars ya nakalto kakakin hukumar kare hakin bil-adama ta MDD cikin wani rahoto da ya fitar a wannan talala, ya ce hare-haren wuce gona da iri da kawancen saudiya ke kaiwa kan al'ummar kasar Yemen ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 136 cikin makuni biyu kacal na baya bayan nan.

Wannan alkaluma da Hukumar kare hakin bil-adama ta Majalisar dinkin Duniyar ta fitar bai shafi na ranar 6 ga watan Satumbar da ya gabata ba.

Tun a watan Maris din 2015, kasar Saudiya bisa cikekken goyon bayan Amurka da wasu kasashen Larabawa suka fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Al'ummar kasar Yemen tare da killace kasar, ta kasa, ruwa da kuma ta sama.

Bayan lashe rayukan duban Mutane, harin yayin sanadiyar jikkatar wasu gomomin dubai na fararen hula tare kuma da raba wasu milyoyi da mahalinsu, bayan ga hakan, a halin da ake ciki, kasar Yemen na fuskantar tsananin karamcin abinci da tsabtaceccen ruwan sha, tare kuma da cutar kwalara.