An Nada Shugabar Asusun Kula Da Kananen Yara Na MDD UNICEF
An nada Henrietta Fore 'yar kasar Amurka shugaban Asusun kula da kananen yara na Majalisar Dinkin Duniya.
A daren jiya juma'a ne aka zabi Henrietta Fore mai shekaru 69 da haihuwa 'yar kasar Amurka a matsayin sabuwar shugabar Asusun kula da kananen yara na MDD wacce ta maye gurbin Anthony Lake da ya jagorancin asusun tun daga shekarar 2010.
Mai magana da yawun sakatare janar na MDD ya bayyana cewa shekaru 40 da suka gabata zuwa yanzu Henrietta Fore ta kasance cikin hidima ga al'ummar Amurka da kuma wasu cibiyoyin fararen hula na kasar.
Babban sakatare janar na majalisar dinkin duniya ya yi ishara da cewa kashi hudu cikin dari na wannan hukuma na a hanun mata ne, domin haka wannan nadi zai kara bawa matan karfin gwiwa wajen ci gaba da ayyukansu kamar yadda ya kamata.