Faransa Ta Hallaka Masu Da'awar Jihadi 10 A Mali
(last modified Thu, 15 Feb 2018 05:51:09 GMT )
Feb 15, 2018 05:51 UTC
  • Faransa Ta Hallaka Masu Da'awar Jihadi 10 A Mali

Majiyoyin tsaro a Mali, sun ce a kalla mayakan dake da'awar jihadi goma ne suka hallaka a wani harin sama da na kasa da sojin Faransa suka kai a arewacin Mali.

Bayanan sun ce an kai harin ne jiya Laraba da nufin hallaka dan asalin kasar Mali nan, Iyad Ag Ghaly wanda shi ne jagoran kungiyar Ansar Dine mai da'awar jihadi a yanki.

Rundinar sojin Mali ta ce daga cikin wadanda aka hallaka a farmakin har da wani tsohon Kanal na sojan Mali, mai suna Malick Ag Wanasnat, wanda yake na hannun daman jagoran mayakan ne dake ikirari da sunan jihadi.

Wata majiyar tsaro daga kasashen waje dake Mali, ta ce an kai harin ne a sansanin da jagoran mayakan Iyad Ag Ghaly, ya ke, a ''Tinzautene'' dake kusa da yankin Inaghalawass a nisan kilomita 900 dage Aljeriya. 

Kungiyar Ansar Dine wacce reshen Al'Qaida ce a yankin na daga cikin gungun 'yan tada kayar baya da suka kwace ikon arewacin Mali tsakanin 2012 zuwa 2013, kafin Faransa ta kaddamar da hare haren murkushe 'yan ta'addan.