MDD Ta Bukaci A Aiwatar Da Kudirin Tsagaita Wuta A Siriya
(last modified Mon, 26 Feb 2018 11:19:11 GMT )
Feb 26, 2018 11:19 UTC
  • MDD Ta Bukaci A Aiwatar Da Kudirin Tsagaita Wuta A Siriya

Babban sakataren MDD, Antonio Guteress, ya bukaci da a aiwatar da kudirin tsagaita wuta a Siriya da kwamitin tsaron MDD ya amince da shi a ranar Asabar da ta gabata.

Mista Guteress ya ce, ya yi maraba da amincewa da kudirin da kasashen mambobin kwamitin tsaro suka amunta da shi na tsagaita wuta ta tsawon kwanaki 30 a Siriya, amma yana bukatar a aiwatar da shi ba tare da wata wata ba.

An dai cimma kudirin ne don bada damar kai daukin gaggawa da isar da kayan agaji a yankin gabashin Ghouta inda dakarun gwamnatin Siriya suka kaddamar da farmaki kan 'yan ta'adda masu samun dauki daga kasashen ketare, biyo bayan harba daruruwan makaman roka da suka yi ta yi a cikin 'yan kwanakin nan a kan birnin Damascus fadar mulkin kasar ta Syria, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da kuma jikkatar wasu.

Kafofin yada labarai na kasashen da suke da alaka da masu tayar da kayar bayan a Syria, e sun nakalto daga majiyoyin masu tayar da kayar bayan da ke dauke da makamai cewa; hare-haren sojojin gwamnatin Syria a yankunan da suka kafa tungarsu a yankin Ghouta ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 450, wanda hakan kuma ya hada da fararen hular da suke yin garkuwa da su da kuma mayakan 'yan ta'addan, wadanda akasarinsu ba 'yan kasar ta Syria ne ba.

 Bayanai daga kasar dai sun ce har yanzu ana gwabza fada duk da kudirin tsagaita da kwamitin tsaro ya cimma.