An Sake Dage Zaben Shugaban Kasar Venezuela
(last modified Fri, 02 Mar 2018 06:32:42 GMT )
Mar 02, 2018 06:32 UTC
  • An Sake Dage Zaben Shugaban Kasar Venezuela

Hukumar zaben kasar Venezuela ta sanar a jiya alhamis cewa; Bayan cimma matsaya a tsakanin gwamnati da wasu jam'iyyun adawa an dage lokacin zaben da wata daya

Hukumar zaben kasar ta ci gaba da cewa; Maimakon ranar 22 ga watan April da za a yi zaben shugaban kasar an dage shi zuwa tsakiyar watan Mayu.

A ranar talatar da ta gabata ne shugaban kasar Nicolas Maduro tare da jagoran 'yan hamayya Henri Falcon,sun shelanta kawukansu a matsayin yan takarar shugaban kasa.

Kawannin da suka gabata, kasar ta Venezuela ta fuskanci rikice-rikicen siyasa, inda 'yan hamayya suka rika yin kira ga shugaba Maduro da ya sauka daga kan mulkin kasar.

A daya gefen gwamnatin Amurka ta kakkabawa gwamnatin Maduro takunkumi da zummar yin matsin lamabar da zai kai ga faduwarta.