Kungiyar Yahudawan Amurka Ta Jinjinawa Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya
(last modified Tue, 03 Apr 2018 17:20:09 GMT )
Apr 03, 2018 17:20 UTC
  • Kungiyar Yahudawan Amurka Ta Jinjinawa Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya

Kungiyar yahudawan Amurka da aka fi sani da American Jewish Committee (AJC) ta bayyana jin dadi dangane da kalaman da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bn Salman yayi na hakkin da sahyoniyawa suke da shi na kafa kasarsu a Palastinu inda ta jinjina masa kan wannan kalami na sa.

Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya bayyana cewar kungiyar yahudawan ta AJC ta bayyana hakan ne cikin wani sako da ta buga a shafinta na  Twitter inda tace: Muhammad bn Salman, Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya fadi wata magana abar jinjinawa wacce babu wani shugaban Saudiyya da ya taba fadi tsawon shekaru 70 din da suka gabata, wacce ita ce kuwa cewa Isra'ilawa suna da hakkin mallakar gwamnati da kasarsu.

Don haka kungiyar ta bayyanar da farin ciki da kuma jinjinawarta ga Yariman na Saudiyya kan wannan kalami nasa.

A jiya ne dai Yarima Muhammad bn Salman din, cikin wata hira da yayi da mujallar The Atlantic  ta kasar Amurka inda ya ce Isra'ilawa suna da hakkin mallakar kasar su a Palastinu, yana mai cewa akwai manufofin da kasashen larabawan Tekun Fasha suka yi tarayyar da Isra'ila wanda za su iya amfanuwa da junansu, lamarin da al'ummomin larabawa da wasu masanansu suke ta Allah wadai da Yariman kan wadannan maganganu nasa.