UNICEF Ya Bukaci A Taimakawa Yaran Zirin Gaza
Asusun dake kula da kananen yara na MDD wato UNICEF ya bukaci a kawo dauki kan kananen yaran Palastinawa a yankin Zirin Gaza.
Cikin wani bayani da ta fitar a wannan laraba, babban daraktar dake kula da asusun yara na MDD a a gabas ta tsakiya da arewacin Afirka ta ce a farmakin da jami'an tsaron Isra'ila suka kaiwa Palastinawa masu zanga-zanga cikin kwanaki goma da suka gabata, kananen yara uku ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama na daban suka samu mumunan rauni.
A yayin da yake alawadai da cin zarafin kananen yara, jani'in ya bayyana cewa shekaru da dama kananen yaran Palastinawa a zirin Gaza ke cikin mawuyacin hali, kuma idan aka yi la'akari da adadin kananen yaran da ya kai dubu 250 a Gaza, a duk cikin yara 4 akwai yaro guda da yake bukatar taimakon tallafi da karfafa masa gwiwa.