UNICEF Ya Bukaci A Taimakawa Yaran Zirin Gaza
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29816-unicef_ya_bukaci_a_taimakawa_yaran_zirin_gaza
Asusun dake kula da kananen yara na MDD wato UNICEF ya bukaci a kawo dauki kan kananen yaran Palastinawa a yankin Zirin Gaza.
(last modified 2018-08-22T11:31:41+00:00 )
Apr 11, 2018 11:15 UTC
  • UNICEF Ya Bukaci A Taimakawa Yaran Zirin Gaza

Asusun dake kula da kananen yara na MDD wato UNICEF ya bukaci a kawo dauki kan kananen yaran Palastinawa a yankin Zirin Gaza.

Cikin wani bayani da ta fitar a wannan laraba, babban daraktar dake kula da asusun yara na MDD a a gabas ta tsakiya da arewacin Afirka ta ce a farmakin da jami'an tsaron Isra'ila suka kaiwa Palastinawa masu zanga-zanga cikin kwanaki goma da suka gabata, kananen yara uku ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama na daban suka samu mumunan rauni.

A yayin da yake alawadai da cin zarafin kananen yara, jani'in ya bayyana cewa shekaru da dama kananen yaran Palastinawa a zirin Gaza ke cikin mawuyacin hali, kuma idan aka yi la'akari da  adadin kananen yaran da ya kai dubu 250 a Gaza, a duk cikin yara 4 akwai yaro guda da yake bukatar taimakon tallafi da karfafa masa gwiwa.