Apr 17, 2018 05:02 UTC
  • Macron Da May Sun Fuskanci Fushin 'Yan Majalisun Kasashensu Kan Harin Siriya

'Yan majalisun kasashen Faransa da Birtaniyya sun tutsiye da kuma nuna fushinsu ga Emmanuel Macro, shugaban kasar Faransan da kuma Theresa May, firayi ministan Birtaniyyan sakamakon harin da suka kai kasar Siriya ba tare da izinin MDD ko kuma alal akalla izinin majalisun kasashen na su ba.

Tashar talabijin RT ta kasar Rasha ta ba da rahoton cewa a zaman da 'yan majalisar Birtaniyyan suka gudanar a jiya Litinin da dama daga cikin 'yan majalisar sun nuna tsananin fushinsu dangane da yadda firayi ministan kasar, Theresa May, ta yi gaban kanta wajen hada kai da Amurka da Faransa wajen kai hari kasar Siriya a ranar Asabar din da ta gabata.

Yayin da yake magana kan hakan, shugaban jam'iyyar Labour, babbar jam'iyyar adawa ta Birtaniyya Jeremy Corbyn cikin fushi ya shaida wa firayi minista May cewa tana  karkashin kulawar majalisar ne ba karkashin umurnin shugaban Amurka ba, yana mai cewa wajibi ne ta nemi izinin majalisar kafin kai hari wata kasa.

A kasar Faransan ma 'yan majalisar kasar, a zaman da suka yi jiya Litinin don tattauna batun harin kasar Siriya, da dama daga cikin 'yan majalisar sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da matsayar da shugaban kasar Emmanuel Macron ya dauka na yin gaban kansa wajen kai hari kasar Siriyan wanda wasu suka ce shugaba Macron din yayi hakan ne don dadadawa Amurka rai, ba tare da wata kwakwarar hujja ta cewa gwamnatin Siriya ta yi amfani da makamai masu guba ba.

 

Tags